27 Disamba 2021 - 14:25
​Desmond Tutu Ya Rasu Yana Da Shekara 90 A Duniya

Fitaccen malamin addinin kirista nan wanda ya yi yaki da wariyar launin fata a Afrika ta Kudu, kana mai kyatar zaman lafiya ta Nobel, Archbishop Desmond Tutu, ya rasu yana da shekara 90 a duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya sanar da rasuwar tasa cikin wata sanarwa a wannan Lahadin.

Ba’a dai bayyana dalilin mutuwar tasa ba, saidai an ce ya rasu a wani asibiti dake birnin Captown.

Tuni dai kasashen duniya suka fara aikewa da sakon ta’aziyya game da mutuwar malamin.

Firaminitan Biritaniya, Boris Jonson, ya wallafa a shafinsa na twitter cewa za’a rika tunawa da dattakon da Archbishop Desmond Tutu ya rayu da shi a tsawon shekaru.

Shi kuwa shugaba Emanuel Macron na faransa cewa gwagwarmayar Desmon Tutu, za ta tsaya a tunaninmu.

342/